Monday, 17 September 2018

An tsinci gawar Manjo Janar Idris Alkali -sojan Najeriya da bace kwanakin baya

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni ne da cewa babban jami'in sojan Najeriyar nan watau Manjo Janar Idris Alkali da muka baku labarin bacewar sa a kwanan baya an tsinci gawar sa.


Mun samu cewa dai an tsinci gawar sojan ne a garin Jos ta jihar Filato a kusa da asibitin koyarwa ta jami'ar tarayya dake jihar akan hanyar zuwa matsugunnin jami'ar na din din din.

Jami'an tsaron Najeriya ne suka gano gawar ta sa tare da wasu masu sana'ar adai-daita a cikin wani kududdufi dake a garin.

Haka zalika dai majiyar tamu tace ana kyautata zaton 'yan kabilar Birom ne dake a jihar suka kashe su duk da yake dai har yanzu ba samu wani bayani ba daga hukumar sojin kasar game da lamarin.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment