Friday, 28 September 2018

Ana ce min ina tafiyar hawainiya: Masu saurin ina suka je?>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna kasar Amurka, shugaban dai na kasar Amurkane inda yake halartar taron majalisar dinkin Duniya, a yayin ganawar tasu, Buhari ya bayyana cewa ana kiranshi da Baba go slow, watau me tafiyar hawaniya.
A wata sanarwa da me magana da yawun shugaban, Femi Adesina ya fitar, Yace amma wadanda suka yi saurin suna ina, ina sukaje?

Ya bayar da misalin titunan da yayi lokacin yana shugaban PTF daga Legas zuwa Abuja da kuma daga Onitsha zuwa fatakwal wanda yace tun shekarar 1999 har zuwa shekarar 2015 ba'a sake yin wani titinba.

Yace amma manyan kasarnan basu ce komai ba akai.

Ya kuma yi alkawarin muddin ya sake cin zaben 2019 to zai yi kokarin kawo canji.

Shugaba Buhari ya kuma karfafawa mazauna kasar ta Amurka dawowa gida dan taimakawa mutanen yankunansu, musamman ta bangaren ilimi inda yace idan mutane suka samu ilimi ba zasu yadda da duk wani shirme ba

No comments:

Post a Comment