Thursday, 27 September 2018

Ana tilasta wa iyaye mata kashe jariransu masu nakasa

An yi ta fadakarwa a kan kawo karshen nuna wa masu nakasa kyama
Wani sabon bincike ya gano cewa ana tilastawa kusan rabin iyaye mata a Kenya da ke da jarirai masu nakasa su kashe su.


Binciken wanda kungiyar da ke kare hakkin masu nakasa suka kaddamar suka kuma dauki shekaru biyu suna yin sa, ya gano cewa ana zargin iyayen ke jawo halin da yaran ke ciki.
Fiye da kashi biyu bisa uku na iyaye mata da aka yi hira da su, sun ce ana ganin yara masu nakasa a matsayin wani bala'i.
Sun gaya wa masu bincike cewa ana zargin su da aikata zunubi - kuma su suka jawo wa kansu.
Daya daga cikin matan ta ce kakarta ta ba ta shawarar ta caccaka wa danta allura cikin jijiyoyinsa don ya mutu. Wata kuma an umarce ta ta bai wa dan guba.
Binciken dai bai bayyana yawan iyayen da suka kashe jariransu masu nakasa.
Amma an shaidawa wa BBC cewa ana yin wadannan kashe-kashen ne a boye shi yasa ba a jin labarin.
Yawancin al'ummomi a fadin duniya da iyaye ke kashe 'ya'yansu a baya sun daina.
Kuma hakan abu ne da ba ya bisa doka a Kenya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment