Thursday, 13 September 2018

Anya Oshiomhole na da cikakken hankali kuwa?>>Jonathan ya tambaya

Tsohon shugaban kasa Goodluck jonathan ya saka alamar tambaya a kan lafiyar hankalin shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole. Jonathan na wannan kalami ne a matsayin martini ga kalaman Oshiomhole na cewar a lokacin mulkinsa ne aka fara amfani da kudi domin sayen kuri’ar masu zabe.


A wani jawabi da Jonathan ya raba ga manema labarai yau, Laraba, a Abuja ya ce bai san dalilin da yasa Oshiomhole zai yi kalaman karya a kansa ba. Tsohon shugaban kasar ya ce Oshiomhole na yin barin zance ne saboda matsalolin da suka dabaibaye ofishinsa.

Jonathan ya ce an fara sayen kuri’un masu zabe ne a zaben jihar Edo na 2016, shekara daya bayan ya bar ofis.

“Ni ina ganin ya rude ne, domin zai yabe ka a yauidan kana APC amma gobe ya kushe ka gobe idan ka fita daga jam’iyyar .

“Hatta ‘yan jam’iyyarsa bai kyale ba domin ko a yanzu haka akwai matsala tsakaninsa da wasu manyan jami’an gwamnatin APC irin su ministan kwadago, Chris Ngige. Halayensa kadai sun isa su rusa jam’iyyar APC,” a cewar kalaman na Jonathan da mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Ikechukwu Eze, ya saka hannu a kai.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment