Sunday, 9 September 2018

APC ce zata lashe zaben 2019 saboda babu wani dan takarar azo a gani da zai akayar da ita>>Lai Muhammad

Ministan labarai da al'adu Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce zata lashe zaben shekarar 2019 me zuwa idan Allah ya kaimu, ya ce dalili kuwa shine babu wani abokin hamayya me kwari da zai iya kayar da jam'iyyar  a yanzu.


Lai Muhammad ya kara da cewa, jam'iyyar PDP ce ya kamata ta samar da dan takara da zai kara da na APC amma matsalar shine tana cikin rudani.

Yace, mutane zasu yi zabene bisa lura da irin ayyukan da gwamnati ta yi musu dan haka yana da yakinin APC ce zata lashe zaben saboda ayyukan raya kasa da ta yi a shekaru uku da ta kwashe tana mulki, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment