Wednesday, 26 September 2018

Ashe Luka Modric dan gudun hijirane?

Bayan da Croatia ta samu nasara a kan Ingila a gasar cin kofin duniya a wannan shekara, an tambayi wani dan Crotia mai sha'awar wasan kwallon kafa kan yadda yake tunanin kasar za ta fuskanci Faransa a wasan karshe na gasar.


''Ka san Luka Modric ko? Ya yi wasan kwallon kafa inda yake ratsa nakiyoyi da aka binne a kasa ma. To kamar shi , mu ma nan ba ma tsaro,'' In ji mutumin

Yaron da yaki ya tagayyara

Shi da wasu da dama daga cikin 'yan wasan kasar Croatia, mutumin da ya ci lambar gwarzon hukumar kwallon kafa na shekara, yaro ne da ya ga bala'in yaki.

A bikin bayar da lambar yabo a babban dakin taron Royal Hall Festival da ke Landan, inda ya karbi kofin, ya sha bam-bam da rayuwar yakin da ya fuskanta sakamakon rugujewar kasar Yugoslavia a shekarar 1991.

Fada ya barke bayan Slovenia da Croatia sun ayyana samun 'yancin kansu, daga nan dakarun Yugoslav/Serbia suka mayar da martani.

Modric, kamar yawancin yara sa'o'in shi ya kasance dan gudun hijirar rikicin bangaranci kuma ya yi rayuwa irin ta 'yan gudun hijira.

Duk da cewa ba lalle ba ne lokacin da Modric yana yaro ya yi tamola a wurin da aka binne nakiyoyi lokacin yakin, to amma ya rika jiran lokacin da sojojin Serbia ke dakatar da ruwan bama-baman da suke yi, sannan ya fito shi da abokansa suna buga tsohuwar bal a kan titunan tashar jiragen ruwa ta Zadar da ke Crotia.

Rashin da ya yi da kuma hadarin da ya shiga
A lokacin ya taso ne cikin rayuwa ta jure wa rashin kakansa kuma mai kula da shi, wanda mayakan sa kai na Serbia suka kashe, da kuma kona gidansu.

A lokacin ana gargadin yara da kada su kuskura su yi nisa daga dakunansu na gudun hijira, kuma su guji zuwa kusa da wani abu da zai iya zama wani tarko da aka dana bam.

''Shekarata shida kawai a lokacin wanda wannan mawuyacin lokaci ainun. Ina iya tuna komai da ya faru a lokacin sosai.'' in ji Modric a shekara ta 2008, a wani lokaci da yake magana a kan yakin.

'Yaki ya karfafa min zuciya'

"Yakin ya kara min karfi. Ba na so in ta tunanin wannan har abada, amma ba na so in manta da shi."

A matsayinsa na dan Crotia Modric dan kasar da take da yawan mutane miliyan hudu da dubu dari ne, wanda hakan da kadan ya dara mutanen birnin Los Angeles na Amurka.

A wannan bazarar kasar ta kasance mafi kankanta da ta kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya tun bayan Uruguay wadda ta je a shekarar 1950.

Yadda aka fi su yawa
Wannan nasara tare kuma da kokarin da kasar ta yi na zuwa matsayi na uku a gasar 1998, ya sa ta wuce matsayin yadda girmanta yake sosai a gasar kwallon kafa.

Mutane da dama suna ganin ta kai ga wannan nasara ne sakamakon irin mawuyacin halin da ta shiga na yaki.

A ranar wasan kusa da karshe na kofin duniya na wannan shekara da Crotia za ta yi da Ingila wata jaridar Crotia mai suna Jutarnji ta yi wani sharhi wanda a cikinsa take kira ga 'yan wasan kasar da su yi gwagwarmaya iyakar iyawarsu tare da hadin kai.

"Hatta kanan kasashe wadanda aka fi su yawan jama'a za su iya yin suna idan suka hada kai suka yi aiki tare," in ji sharhin.

To amma kuma tsananin kishin kasa na 'yan Crotia, da kuma irin wahala da azabar da suka sha ta neman 'yanci, sun sa musu kishin kasa wanda a wani lokaci yake zama maras kyau
Bayan da 'yan wasan kasar suka doke 'yan Argentina 3-0 a wasan matakin rukuni-rukuni na cin kofin duniya, an jiyo wasu daga cikin 'yan wasan a dakinsu na sanya tufafi suna wata wakar kishin kasa ta mayakan sa-kai masu ra'ayin rikau a Crotia.

Duk da irin ce-ce-ku-ce da a wani lokaci ke tattare da irin tsananin kishin kasa na 'yan Crotia, kasa ce da har kullum take matukar alfahari da nasarorinta a fagen wasanni.

Babu ma dai kamar lokacin da Luka Modric ya daga kofin zama gwarzon dan kwallon hukumar kwallon kafa ta duniya a ranar Talata da daddare.
BBChausa


No comments:

Post a Comment