Wednesday, 26 September 2018

Asirin Wasu Manya A Kasar Nan Zai Iya Tonuwa Idan Har Rikici Tsakanin Shahararrun Mata A Kafafun Sadarwa, Wato Jaruma Empire Da Layla Ali Othman Bai Kawo Karshe Ba

Rikici ya barke tsakanin wasu sanannun mata na kafafun sadarwar zamani wato Hauwa Sa'idu Muhammad wadda aka fi sani da Jaruma Empire da kuma Lalya Ali Othman.


A wani bidiyo na mayar da martani da Jaruma Empire ta fitar, an ga tana yi wa Layla Ali zagin kare dangi bisa yawan hannunka mai sanda da take yi mata a shafin sadarwa na Instagram, wanda hakan bai yi mata dadi ba.

Jaruma Empire wadda babbar kawa ce ga Rahma Indimi, ta kuma kara da fallasa yadda Layla take sharholiya da manyan mutane, inda a bidiyon da ta fitar har da zargin Layla na da alaka da Sanata Abdul Ningi, wanda a cewar ta an jima ana zargin tana tarayya da Sanatan.

Babbu shakka idan har rikicin da ya bullo tsakanin Jaruma Empire da Layla Ali Othman bai kawo karshe ba, za su iya tonawa wasu manyan kasar nan dake sharholiya da 'yan mata asiri, ganin yadda kowacensu ta daura damara domin amayar da abin da ya jima a boye a tsakaninsu.
Rariya.

No comments:

Post a Comment