Wednesday, 12 September 2018

Atiku ya caccaki Buhari a ziyarar da ya kai Kano

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kaca-kaca gami da sukar jam'iyya mai ci ta APC kan watsi da kudirinta na sauya fasalin kasa.


Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan cikin babban birni na Kanon Dabo yayin ganawarsa da manema labarai a kwana-kwanan.

Turakin na Adamawa wanda yana daya daga cikin wadanda suka bayar da muhimmiyar gudunmuwa ta kafa tsare-tsaren sauya fasalin kasar nan tare da yi ma ta garambawul tun a shekarar 1994, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan watsi da wannan kudiri.

Atiku ya kausasa harshe tare da bayyana damuwarsa kan wannan lamari sakamakon rashin cika alkawarin da gwamnatin shugaba Buhari ta kudirta yayin yakin ta na neman zabe a shekarar 2015.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment