Wednesday, 19 September 2018

Auren kashe wuta: Ya faru da gaske

Wannan labarin da zaku karanta gaskiyane ya faru ba kirkira bane, saidai an boye sunan garuruwan da ya faru da kuma  ainihin sunayen mutanen da abin ya faru dasu.

Ana saura kwana daya a daura auren lawal da bilkisu, lawal ya gayyato abokanshi itama amarya haka suka hadu a gurin shakatawa.

Saidai bilkisu kwata-kwata fuskarta a murtuke take saikace wadda aka aikowa da sakon mutuwa.


Suna zaune ita da ango a tsakiya da wata kawarta a kusa da ita yayin da sauran abokan ango da kawayen amarya suka sasu a gaba za'a fara sha'ani, sai kawai Bilkisu ta kalli babban abokin ango, me suna Sani tace yazo, ta ce kawarta dake kusa da ita ta tashi, tace Sani ya zauna kusa da ita.

Abin ya daurewa Sani kai saboda duk da yana babban abokin ango amma be taba ganin Bilkisu ba sannan wannan abu da tayi zai iya saka alamar tambaya a zukatan mutane.

Nan Sani yace mata 'a'a ba za'ayi hakaba ki yi hakuri ku zauna da kawarki'

Atafau Bilkisu tace ita sam sai Sani ya zauna kusa da ita, shi kuma Sani tunanin abinda zaije yazo yasa yaki zama.

Nan amarya, Bilkisu ta tashi ta tafi can gefen wani ruwa dake a gurin shakatawar ta zauna tana kallonshi.

Wasu daga cikin kawayenta da ango suka zo gurinta amma tace duk su tafi bata son ganin kowa sai Sani, akai-akai da ita tace, 'Nifa wallahi babu wanda zan saurara sai Sani'

Nan aka kira Sani yazo, dole ba dan yana so ba ya zauna kusa ita, ya fara mata tambayar wai ke a ina kika sanni? Kuma me yasa kike haka? tace babu komai kawai taga ya birgetane tace ya zo su zauna.

Sani yace 'amma kinsan mutane zasu iya tunanin wani abu koh, musamman ga wanda zai aureki abokinane'

Bilkisu tace su yi tanuninsu ni ba damuwata bace.

Sani yace mata ' dan girman Allah yanzu ki tashi kije a ci gaba da abinda ya kawomu'

Bilkisu tace ' indai ba zaka yadda ka zauna kusa dani ba ni kuma wallah an tashi kenan bazan koma ba'

Sani yaga da gaske take, sai yace mata yana zuwa, yaje ya samu abokinshi ango yace kaji-kaji abinda ke faruwa.

Ango yace, abokina kace mata ka yadda tazo muyi abinda zamu yi a sallami mutane.

Haka Sani ya koma suka taso tare da Bilkisu suka nufo gurin kamar shine angon, yanzu fuskarta a sake take.

Suka zauna shi da Ango, Lawal suka saka Bilkisu tsakiya. A haka aka gama abinda za'ayi aka watse.

Washe gari bayan daura aure, irin yamma ta dan fara yi sai ango da abokanshi suka tafi gidan su amarya, saboda ya shirya wani shagalin har ya kama babban dakin taro da za'ayi.

Isarsu kofar gidan su amaryar ke da wuya, tunda ta kyallara ido ta gansu kawai sai ta fasa kururuwar ' na fasa wallahi banyin auren, ya zo ya bani takar data'.

Abokan ango suka rike baki cikin mamaki, ita kuwa Bilkisu kururuwarta taci gaba da yi tana zage-zage, ta inda take shiga ba nan take fita ba.

Kowa ya kasa shawo kanta.

Sai akace to Babban abokin Ango Sani yaje aga ko zata saurarreshi, Sani na zuwa  cikin sanyin murya yace mata 'haba amarya ke kuma irin wannan rana ta farin ciki haka sai kibi ki tayar da hankalinki'

Menene matsalar?

Bilkisu tace 'takalmine nace ya siyo min amma tun tuni yaki ya saimin da kuma kudin da nike so ya bani yana ta wani ja min rai'

Sani yace 'matsalar kenan, idan aka sai miki zaki yadda mu tafi? Tace 'Eh'

Sani ya cire kudin da tace tana bukata ya bata, sannan yace mata ' ko kinsan nawa ake saida takalmin'?

Ta gaya mishi, yace 'ko shima in baki kudin kawai'? Tace 'Eh' 

Duk Sani ya bata aka kammala komai ta shirya zasu tafi gurin shagalin biki, an ware mata mota ita da ango amma tace atafau ita motar da Sani yake zata shiga

Nan dai aka ce ta shiga suje.

Anje gurin shagali Amarya da ango suna zaune sai ta kira Sani a nan ma tace ya zo ya zauna kusa da ita, Sani yace, 'a'a kinga nan ni ke kula da baki da kuma sauran abubuwa dan su tafi daidai, dan haka kiyi hakuri ki zauna'

Da kyar ya shawo kanta ta yadda ta zauna amma tace saidai ya zauna a kujerar dake saitinta ta gaba inda zata rika ganinshi sannan kuma tace duk lemukan da aka shirya a teburinta ita da ango ya kwashe ya zuba a gabanshi.

Haka kuwa akayi.

Ana tsaka da sha'ani sai amarya, Bilkisu tace, tana jin fitsari, wata abokiyarta ta rakata waje da niyyar yin fitsari.

Ashe sun shirya tuggu, tun daga gida sun hada zobo da laya a ciki sunzo dashi.

kawai sai suka zuba a jikin amaryar da layar, da yake dare yayi babu wanda zai tsaya tantancewa, anan suka kurma ihu' Amarya tayi aman jini hadda laya'

Da yake inda suka je fitsarin ba kusa da dakin taron bane kuma da hayaniya a cikin dakin taron, ba'a jisu ba.

Sai da Sani abokin ango yaga sun dade basu dawo ba sai ya bi sahu, ai kuwa yana zuwa yaga amarya da kaya jajawur ga laya.

Nan suka bashi labarin cewa, wai tsohon mijintane ya mata sihiri gashi ta yi aman jini hadda laya.

Nan Sani ya koma ya kira Ango gefe ya sanar dashi abinda ake ciki, anan suka yi shawarar cewa kada a bari mutanen gurin taron su sani kawai su dauketa su yi Asibiti da ita.

Haka kuwa akayi, saidai ana kan hanyar zuwa Asibiti, Bilkisu tace kada a kaita Asibiti a kaita gida.

Nan suka ce yaya haka?

Tace 'na warke a kaini gida'.

Dole suka juya mota aka yi hanyar gidan su Amarya.

Ana zuwa ta falle wuka tace wallahi ta fasa auren kawai ya bata takardar 

'Kada wanda ya sake yazo kusa dani'

A haka akaita fama da amarya Bilkisu hadda iyaye da 'yan uwa duk an kasa shawo kanta, to da yake ba'azo da Sani ba duk suka rasa yanda zasu yi da ita.

Can sai ga Sani ya karaso gurin.

Yana zuwa tace 'Yawwa Sani kai kadaine mutumina, sauran duk 'yan kan abin ubane'

Sani ya karasa kusa da ita yana dari-dari, yace 'ajiye wukar dan Allah' 

tace 'kada ka damu aikai nawane zan rike tane saboda tsaro, koda wani zai zagayo ta baya'

Anan ya rika rarrashinta akan tayi hakuri a kaita dakin minjinta amma tace 'wallahi ba zata ba tun yau ta fara ganin tashin hankali'

Nan ya gaji da rokonshi ya tashi ya kyaleta saboda dare na kara yi.

A haka aka watse bata tare ba a ranar.

Washe gari 'yan jarida suka ji labari suka zo gidan, koda zuwansu suka tambayi Bilki akan abinda ya faru sai ta bayyana cewa ita bata san duk abinda ya faru ba dama tana da Aljanu kuma ita tana son mijinta yanzu ma ta kagara a kaita gidan mijinta.

Da akaji haka akace to shikenan ai dama haka akeso, kawai aje a kaita gidan mijinta.

Bayan tarewarta, tayi irin girkin farko dinnan, Ango Lawal ya gayyato abokai aci abinci, ya siyo 'yan lemukanshi da zai ba abokai.

Amma sai Amarya, Bilkisu tace babban abokin Ango, Sani kawai zata ba lemu kuma yazo tare da ita zasu ci abinci.

Haka kuwa akayi duk da Sani ya nemi ya kiya da farko, sauran abokan angon kuwa saidai wani lemun aka siyo musu.

Ango Lawal yana zaune ne da Amaryarshi Bilkisu a gida daya da mahaifiyarshi da wanshi.

Bilkisu ta rika ci mai mutunci hadda zagin mahaifiyarshi amma duk da haka ya kasa sakinta duk da tana ta bijiro da bukatar hakan.

Tun yayanshi yana jurewa yana wa Lawal hannunka me sanda akan ya saki Bilkisu har rannan dai aka kaishi bango yace zagin da akewa mahaifiyarshi ya isa haka.

'Kodai ka saki matarnan ko kuma ku tashi ku bamu guri', 

Lawal ya shiga tsaka mai wuya, gashi dai yana son matarshi duk da irin wannan dambarwa data faru.

Sai ya samu babban abokinshi, Sani, ya zayyanamai duk abinda ke faruwa.

Sani yace, 'abokina bani labarin yanda kuka hadu da Bilkisu'.

Lawal yace, kawai ganinta na yi nace ina so, bayan kwana biyu sai ta ce mai zata je  garinsu kuma da ta dawo zasu yi aure.

'Abin ya bani mamaki', Lawal ya gayawa Sani.

'Nace mata daga haduwa kuma sai maganar aure'?

Tace min 'Eh me za'a jira'

'Nace mata yayi wuri'.

'Amma ta hakikance akan haka'

'Dan maganar ta wuce, nace mata shikenan Allah ya dawo dake lafiya'

'Tana dawowa kuwa sai maganar aure ta tashi aka fara hidima'

Sani ya kalli abokinshi Lawal yace 'yanzu kai baka fahimci komai akan wannan abin da ya faruba, duk da irin wulakancin da take maka, tana zagin mahaifiyarka amma duk da haka kana sonta?

Lawal yayi shiru dai baice komai ba.

Sani ya ci gaba 'To wallahi abokina Bilkisu asiri ta maka shiyasa baka ganin duk abinda take maka, kaga ce maka da tayi zata je garinsu, to asiri taje aka yo maka kuma rabuwa da ita kawai shine mafita tunda har tana zagin mahaifiyarka ni banga alfanun zama da ita ba'

Lawal yayi shiru.

Sani yace 'nidai iya shawarar da zan baka kenan'.

Lawal yace 'nagode'. Suka rabu.

A ranar Lawal bai koma gida ba sai can dare yayi sosai.

Ai kuwa ranar ma aka yi sa'a Bilkisu ta fara zazzaga mai, sai maganar da suka yi da abokinshi Sani ta fadomai ' Asiri ta maka ka sake ta kawai'

Nan ya tashi ya kashe ta da mari.

'Ka mareni'? 

'An mareki din'

Sai jikinta yayi sanyi

Yace 'duk abinda kike min yau yazo karshe dan kuwa na gano cewa asiri kika min kika aureni shiyasa ban ganin duk wulakancin da kike min kije na sakeki saki daya'

Wajan karfe daya na darene.

Nan kuwa yayan Lawal yace 'tunda ya sakeki wallahi ba zaki kwana a gidannan ba'

Bikisu cikin sanyin murya tace 'to ina zani cikin dare haka'?

Yace 'wannan matsalarki ce'

'Kuma kada ki sake ki dawo ko kwasar kayanki, da safe zan sa a kawo miki su har gida'

Nan fa ta marairaice a barta ta kwana da safe ta tafi.

Shi kuwa yayan Lawal yace ba zata yiyuba.

Daga karshe dai ya kira 'yan uwanta suka zo cikin daren suka tafi da ita.

Da gari ya waye, da sassafe yayan Lawal yasa aka kira me motar daukar kaya aka kwashe kayan Bilkisu gaba daya aka kai mata su gida

Nan fa aka maka yayan Lawal a kotu saboda kwashewa Bilkisu kaya da yayi ba da saninta ba.

Da aka je kotu alkali ya karantowa yayan  Lawal laifinshi.

Yayan Lawal ya amsa laifinshi sannan yace 'Wallahi bacin raine, irin zagin da akewa mahaifiyarshine ya isheshi shi yasa ya aikata haka amma yana bayar da hakuri'

Alkali yace tunda be wahalar da shari'a ba za'a yankemai tara ya biya.

Aka yanke tara ya biya.

Karshe zaman Lawal da Bilkisu kenan.

Me karatu zaka/ki iya aiko da labarinka/ki ko na wani daka shaida ya faru a gaske da ka/ki ke tunanin ya kamata mutane su sani dan ya zama darasi ga na gaba.

Aiko ta wadannan hanyoyi kamar haka:
hutudole@gmail.com
Ko sako ta waya a wannan lambar: 08056996072.

1 comment: