Thursday, 13 September 2018

Ba na tsoron karawa da Kwankwaso>>Shekarau

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya daura aniyyar tsayawa takarar dan majalisar dattijai na Kano ta tsakiya, kujerar da a yanzu tsohon gwamna Sanata Rabi'u Kwankwaso yake kai.


Sanata Kwakwaso dai ya koma PDP daga APC da aka zabe shi, kuma a yanzu yana neman takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar.

Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya koma APC sabo da mika wa kwakwaso shugabancin jam'iyyar PDP a Kano, ya ce APC ce ta yi masa tayin yin takarar kujerar.

Ya ce ya koma APC ba tare da gindaya wasu ka'idoji na cewa ga abin da yake so ba.

"Su da kansu jam'iyya da Kano da kasa suka aiko cewa don Allah ko zan zo in yi takarar dan majalisar dattijai Kano ta tsakiya," in ji Shekarau.

Ya shaida wa BBC cewa tun daga lokacin ya yanke shawarar fita daga PDP ya ajiye sha'awarsa ta yin takarar shugaban kasa.

"Da ma takarar nan a PDP na ke yi, kuma yanzu ba na PDP, don haka wannan zancen takara babu shi," in ji shi.

Shekarau ya ce ba kuma zai soma batun neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba a 2019, sabo da tuni jam'iyyar ta yanke hukuncin cewa Shugaba Buhari ne dan takarar ta.

"Kuma da ma ban shiga cikin APC da wannan kuduri ba," a cewar sa.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa ba ya jin tsoron kara wa da ko waye daga jam'iyyar APC, ko da kuwa Kwankwaso ne zai sake yin takarar.

Ya ce ko da Kwankwason ne zai sake yin takarar, babu wani abin fargaba, a shirye ya ke ya kara ko ma da wanene, "wanda Aallah ya ba wa sai mu ce san barka," a cewar Shekarau.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment