Tuesday, 4 September 2018

Ba Ni Da Halin Biyan Naira Miliyan 55 Kuɗin Fitowa Takara A Jam'iyyar APC.

Shugaba Buhari ya faɗa wa shugabancin jam'iyyar APC ba zai iya biyan kuɗin sayen Tikitin tsayawa  takara ba a APC saboda ya yi masa tsada. 


Shugaban ya kara da cewa, shi fa ɗan albashi ne, ta yaya za yi ya iya cire waɗannan zunzurutun kuɗi har miliyan 55 don sayen tikitin takara a jam'iyya?

Idan ba mu manta ba, shugaban ya taɓa makamancin wannan furuci a game da kuɗin takara a kakar zaɓe na shekarar 2015. Game da kuɗin takarar shugaban kasa a APC Naira miliyan 27 da rabi da yake a da. Bayan cin zaɓen ne, shugaban ya ce zai yi mai yiwuwa don ganin ya sa an rage kuɗin takarar. Sai ga shi kuma an sake ruɓanya waɗannan kuɗaɗe.

 Inda kuɗin Fom ɗin takarar ya yi tashin gwauron zabi izuwa miliyan hamsin, yayin da kuɗin na gani ina so Naira miliyan biyar. Abinda ya ba da jimillar kuɗin takarar zuwa, Naira miliyan 55. 

Bayan haka ma an ruɓanya kuɗaɗen takarar sauran mukaman a Karkashin jam'iyyar kamar haka; kuɗin takarar gwamna, an mai da shi miliyan 22 da rabi saɓanin miliyan 5.5 biyar da rabi da yake a da. Na takarar sanata kuma ya koma 8.5 miliyan takwas da rabi saɓanin miliyan uku da dubu ɗari uku da yake a da. Sai na 'yan majalisar tarayya da ya koma ninki ukun da, wato  daga miliyan biyu da dubu dari biyu (2.2 million) zuwa miliyan shidda da rabi (6.5 million).  Sai na majalisar jaha shi kuma ya tashi daga Naira dubu ɗari biyar da hamsin (550,000), zuwa Miliyan ɗaya da dubu ɗari (1.1 million). 

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar 'yan kwamitin jam'iyyar da alhakin abin ke rataye a wuyansu,  su sake duba yiwuwar yin sassauci musamman ma da wata kungiyar matasa masu son a dama da su a harkar mulki (not too young to run group) ta yi matsin lamba na a sassauta kuɗin domin matasa su samu damar yankar tikitin tsayawa takarkaru a jam'iyyar ta APC. Kamar yadda wani mai magana da yawun kungiyar, Mista Jide Ola ya sanar da 'yan jarida.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment