Thursday, 6 September 2018

Babban Bankin Nijeriya Zai Baiwa Masu Sana'o'in Aski, Faci Da Sauransu Tallafin Naira Bilyan 220

Masu sana'ar aski (Barber) da masu sana'ar Faci, da masu sana'ar gyaran gashi (Hair dressers) da dai sauransu ne za su amfana da shirin bayar da tallafin babban bankin Nijeriya na zunzurutun kudi naira biliyan dari biyu da ashirin (N220bn)


A sanarwar da babban bankin na Najeriya ya bayar wato CBN yace: ya ware zunzurutun kudade akalla naira biliyan dari biyu da ashirin (N220bn) domin tallafawa masu kananan sana'oi karkashin wani tsari da bankin ya fito da shi na tallafawa masu kananan masana'antu. Wanda ake kira a turance da 'Micro Small and Medium Enterprises Development Fund (MSMEDF)'.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment