Saturday, 8 September 2018

Babu inda zanje ina nan a Madrid>>Marcelo

Tauraron dan kwallon kungiyar Real Madrid, Marcelo ya musanta raderadin da ke yawo cewa wai zai bar kungiyar ya bi tsohon abokin wasanshi, Cristiano Ronaldo zuwa Juventus.


Marcelo ya gayawa gidan talabijin na Madrid din cewa, yana nan a kungiyar har zuwa karshen sana'arshi, ya kara da cewa, burishi ya bugawa fitacciyar kungiyar kwallo wasa kuma shi a gurinshi, Real Madrid ce kungiyar kwallo ta daya a Duniya.

No comments:

Post a Comment