Tuesday, 11 September 2018

Bani da miliyan 20 da zan sayi fom din takara

A jiyane kungiyoyin IPMAN, NATO, data 'yan kasuwar Sheikh Gumi dake Kaduna data Daurawa da Kastinawa mazauna jihar suka sayawa gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai fom din tsayawa takara karo na biyu.


Da yake karbar kungiyoyin a gidan gwamnati, Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa bashi da miliyan 20 da zai sayi fom din.

Yace a lokacin da jam'iyya ta bayyana cewa fom din shugaban kasa miliyan 50 ne, shugaba Buhari ne ya fara fadin cewa bashi da miliyan hamsin din da zai sayi fom din, yace, har sun fara magana tsakaninsu, Gwamnoni akan yanda zasu sayawa Shugaba Buharin fom din, sai suka tafi ziyara kasar China.

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa, suna can ne sai ya gayawa Buhari cewa wata kungiya ta saya masa fom din takara, sannan yace to shi kuma sai ya sai mishi nashi.

El-Rufai yace, asusun ajiyarshi guda dayane a bankin GT kuma kudin dake gareshi a ciki basu kai kusa da miliyan 20 ba, kamar yanda Cable ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment