Thursday, 27 September 2018

Buhari Manzo Ne Allah Ya Aikowa 'Yan Nijeriya>>In Ji Dan Majalisar Dokokin Sokoto Hon. Sani Yakubu

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato Hon. Sani Alhaji Yakubu ya bayyana cewar Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari manzo ne Allah ya aikowa al'ummar Nijeriya. 


Dan Majalisar wanda ke neman sake takara domin wakiltar Karamar Hukumar Gudu A Majalisar Dokoki ta Jiha a karo na hudu a jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne a Shirin Tsaka Mai Wuya na Gidan Radiyon Muryar Amurka wanda Aliyu Mustapha Sokoto ke gabatarwa. 

Ya ce "Abin da magoya bayan bayanshi irin su Hon. Gwanda Gobir ba su gane ba shine Buhari fa sakon Allah ne ga jama'ar Nijeriya. Mu mun yadda Allah ne ya aikowa al'ummar Nijeriya Buhari."

Ya kara da cewar "A matsayinmu na 'yan APC, matsayin mu na Musulmai kuma a matsayin mu na 'yan Arewa mun yadda Buhari sako ne daga Allah zuwa ga 'yan Nijeriya." In ji Dan Majalisar. 

Abokin muhawararsa a shirin Tsohon Dan Majalisar Wakilai Hon. Shu'aibu Gwanda Gobir kuma Mai Baiwa Gwamna Tambuwal Shawara ya kalubalanci Dan Majalisar da cewar ya kawo masa aya ko hadisin da suka bayyana lokacin da aka yi wa Buhari wahayi? amma ya kasa. 

Tuni dai al'ummar mazabarsa a Gudu da al'ummar Jihar Sakkwato bakidaya suka fito fili suka yi Allah-wadai da kalamansa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment