Wednesday, 12 September 2018

Buhari Ne Dan Takara Daya Tilo Da Muke Da Shi A Matakin Shugaban Kasa, dan haka babu zaben fidda gwani>>APC

Jam'iyar APC ta kasa ta soke gudanar da zaben fitar da gwani na Shugaban kasa a zaben 2019, APCn ta dakatar da presidential primary election ne saboda dalilai biyu, na farko shine har yanzu ba'a samu wani mutum a jam'iyar ba da ya fito da niyyar shima yana so ya tsaya takaran Shugaban kasa a inuwar jam'iyar.


Dalili na biyu shine, Saboda majalisar 'Koli na jam'iyar sun yanke shawarar tsayar da Shugaba Buhari a matsayin dan takaran Shugaban kasa na jam'iyar a zaben dake tafe, kamar yadda Magatakardar jam'iyar Mai Mala Buni ya bayyana wa manema labarai a Abuja, dan haka Shugaba Buhari ne kadai jam'iyar ta tsayar saboda an rasa Wanda zai tsaya ya yi takara dashi a cikin jam'iyar, abinda ya rage yanzu shine zaben fitar da gwani na gwamnoni zuwa kasa, babu na Shugaban kasa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment