Saturday, 15 September 2018

Buhari ya amince da murabus din ministar kudi:Kalli wadda ta gajeta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da murabus din ministar kudi Mrs. Kemi Adeosun, wacce ta yin jabun takardar yi wa kasa hidima.


Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaba kasar Femi Adesina ya fitar a daren Juma'ar nan.

Femi ya ce shugaban kasar ya kuma amince karamar ministar kasafin kudi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed ta ci gaba da kula da ma'aikatar ta kudi.

Wanan itace sabuwar ministar kudu.

Matakin shugaban kasar ya biyo bayan wasikar da tsohuwar ministar Kemi Adeosun ta tura wa Shugaba Buhari tana bayyana cewa ta yi murabus daga matsayinta, saboda badakalar takardun yi wa kasa hidima ta bogi da ta gabatar.

A wasikar Kemi ta ce ta yanke hukuncin ajiye mukaminta ne domin kare kimar ta da kuma mutuncin gwamnati.

A watan Yuli ne jaridar Premium Times da ake buga wa a internet ta wallafa wani bincike da ya gano cewa, takardun yi wa kasa hidima da tsohuwar ministar ke amfani da su na boge ne.

Batun ya janyo wa gwamnati suka, kasancewar fadar shugaban kasa ta yi shiru a kan batun sannan ba ta dauki mataki ba.

Dokokin Najeriya dai sun tanadi cewa, dole ne duk dan kasar da ya kammala karaun digiri ko babbar diploma ya yi aikin yi wa kasa hidima na shekara guda idan bai haura shekara 30 ba, in kuma ya haura shekara 30 to za a bashi takardar shaidar tsame shi daga wadanda za su yi wa kasar hidima.

Kemi dai ta ce wasu da ta amince da ne suka kawo mata takardar cire ta daga wadanda za su yi wa kasar hidima, kasancewar lokacin da ta koma Najeriya domin ci gaba da zama tana da shekara 34.

Gabanin nan dai, an haife ta ne a Birtaniya, kuma a can ta yi gaba dayan rayuwarta har zuwa lokacin da ta koma kasar ta iyayenta.
BBChausa

No comments:

Post a Comment