Thursday, 13 September 2018

BUHARI ZAI BULAGURO ZUWA AMURKA

Bayan makwanni kalilan da dawowarsa daga kasar Cana, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya daura aniyar tafiya kasar Amurka. Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin ministan  harkokin kasar waje,  Mista Geoffrey Onyema. 


Ya fada yayin zantawar sa da manema labarai jiya a Abuja. Inda ya bayyana cewa, shugaban zai shilla zuwa kasar Amurka ne, domin halattar taron majalisin kasashe da   majalisar dinkin  Duniya ta saba yi a birnin Newyork. Wannan shi ne karo na 73. 

Kuma za a gudanar da taron ne ranar 18 ga watan satumbar shekarar 2018 da muke ciki. Mista Onyema ya kara da cewa, Buhari zai yi amfani da wannan dama don samar wa kansa gurbi na din din din a majalisar. Idan ma an ci sa'a, kasar Najeriya za ta iya samun shugabancin irin wannan taro a karo na gaba. Don haka wannan dama ce da shugaban zai yi amfani da ita domin ya daukaka darajar 
kasar nan a Duniya.

 Ya karkare da cewa, a taron Buhari zai gabatar da matsaloli kamar yadda za fatattaki talauci, da yadda za a samar da zaman lafiya a kasa, da bunkasa tsaro, 'yancin dan Adam da makamantansu.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment