Thursday, 6 September 2018

Canja sheka ba zai bawa masu cin hanci mafaka ba>>Magu

Ibrahim Magu, Shugaban riko na hukumar yaki da rashawa da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya ce canja sheka da 'yan siyasa ke yi ba zai hana hukumar ta cigaba da gudanar da binciken ta a kan yan siyasan ba.


Cikin yan kwanakin nan, wasu na zargin cewa dukkan 'yan siyasan da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress APC, sun tsira daga hukumar EFCC.

Amma a hirar da ya yi da 'yan jarida a Legas jiya Laraba, Magu ya ce babu inda 'yan siyasa da suka sace kudin jama'a za su koma da zai hana hukumar bincikarsu.

"Kawai don dan siyasa ya sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata ba zai hana mu dakatar da binciken da muke akansa ba. Bamu dena bincike sai mun kammala.

"Kotu ne kadai ke da ikon wanke mutane daga zargi muddin an gurfanar dashi a gabanta," inji Magu.

A yayin da yake mayar da martani kan zargin da ake na cewa jam'iyyar APC tana yi masa katsalandan cikin aikinsa, Magu ya ce babu wanda ya taba bashi umurnin ya dakatar da binciken da ya keyi.

"Tun farko ni ba irin mutumin da za'a bashi umurnin ya dakatar da bincike ban," inji shi.

Shugaban na EFCC ya ce yanzu duk wani wanda ake bincike yana fakewa da siyasa ne musamman yanzu da babban zaben 2019 ke karatowa.

Ya kara da cewa kafafen yada labarai suna da muhimmiyar ruwa da zasu taka wajen wayar da kan jama'a saboda baragurbin 'yan siyasa da barayin dukiyar jama'a su dena amfani da siyasa don rudar jama'a.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment