Sunday, 30 September 2018

Ci gaban labarin mijinda ya bi matarshi gadon asibiti suka yi kwanciyar aure a gaban sauran marasa lafiya: Karanta yanda ta kaya da aka kaisu kotu

A kwanakin bayane muka ji labarin wani miji da aka kwantar da matarshi a asibiti a kasar Zimbabwe amma ya kasa hakuri sai da ya bita har gadon asibitin suka yi kwanciyar aure a gaban sauran marasa lafiya.

Andai gurfanar da ma'auratan a gaban kotu, Elton Chitanda dan shekaru 29 da matarshi, Fadzai Chivende 'yar shekaru 25 sun gamu da hukuncin biyan tarar dala 75 kowanensu saboda damun marasa lafiya da suka yi da kuma aikata jima'i a bainar jama'a.

An zargi mijin da sadadawa asibitin wajan karfe 3 na dare inda ya samu matartashi suka yi kwanciyar aure akan gadon asibitin kuma suka damu marasa lafiyar da surutai.

Da ake gudanar da shari'ar, alkalin kotun ya gayawa ma'auratan laifin da ake zarginsu dashi amma sai suka musanta, mijin yace kawai dai yaje ya sameta ne suka rungumi juna suka kuma sumbaci juna amma basu yi jima'i ba.

Alkalin ya koma kan matar ya tambayeta, ke haka aka yi? Sai ta juya ta kalli mijinta sannan ta amsa da Eh.

Duk tambayar da aka musu irin amsar da mijin ya bayar ita matar ke bayarwa, da alkalin yaga haka sai yace kada ta kara kallon mijin nata idan ya mata tambaya, kawai ta rika bashi amsa.

Dadai suka ga an kaisu makura, ma'auratan sun amsa cewa sun dai kwanta akan gadon asibiti suka yi huddodin soyayya amma fa basu yi jima'i ba.

Daga nanne sai alkali ya yanke musu hukunci.

No comments:

Post a Comment