Thursday, 27 September 2018

'Cin amanar juna tsakanin ma'aurata a India ba laifi bane'

Babbar kotun India a yau Alhamis, ta yanke hukuncin cewa aikata laifin cin amanar ma’aurata ko kwartanci ba laifi bane a kasar.


Yayin da take yanke hukuncin soke dokar da India ta shafe sama da shekaru 100 tana aiki da ita, babbar kotun kasar ta ce zartas da hukuncin dauri akan wadanda aka samu da laifin cin amanar abokan zamansu na aure cin zarafin dan adam ne.

A cewar kotun dokar ta baya da aka kafa a zamanin mulkin mallaka, ta tauye mata hakkinsu na ra’ayi ko zabin da ya shafi rayuwarsu, zalika haramtawa matan aure ko magidanta neman wasu ma’auratan da lalata, tamkar mayarda mata dukiya ko kadara ce ga maza.

A karshe babbar kotun ta India ta fayyace cewa matakin cin amanar juna da ma’aurata kan yi da ake kallo a matsayin laifi a baya, a halin yanzu ba laifi bane illa zabi na abinda ya shafi rayuwar dan adam.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment