Wednesday, 19 September 2018

Cristiano Ronaldo ya samu jan kati a wasan farko na cin kofin zakarun turai da ya bugawa juventus

Tauraron dan wasan kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya samu jan kati a wasan farko da ya bugawa Juventus din a kasa da mintuna talatin da fara wasa a wasan da suka buga da Valencia.


Ronaldon ya samu jan kati ne a karon battar da sukayi da dan wasan baya na Valancia, Jeison Murillo inda alkalin wasa ya nuna mishi jan kati da farko Ronldo ya nuna mamakinshi amma daga baya aka nunashi ya rufe fuska, yana kuka.

Sau 154 Ronaldo na buga wasan gasar cin kofin zakarun turai amma be taba samun jan kati ba sai a wannan karin.

Jan katin da ya samu na nufin cewa bazai buga wasan gaba da Juven zasu buga da Young Boys ba da kuma watakila wasan da zasu buga da tsohuwar kungiyarshi ta Manchester United ba, koda yake hakan zai dogara da irin hukuncin kwamitin ladaftarwa na UEFA ya fitar a kanshi.

No comments:

Post a Comment