Tuesday, 11 September 2018

Da mutum ya bude kasuwanci sai a turomai EFCC su tambayeshi ina ya samu kudin? To ni ba haka zanyi ba idan na zam shugaban kasa>>Jonah Jang

Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ya bayyana cewa, burinshi shine zama shugaban Najeriya dan haka ba zai janye wa kowane dan takara ba.


Jang ya bayyana hakane ga 'yan jarida a wani taron da yayi da su a gidanshi dake Maitama, babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda Daily post ta ruwaito, yace ta wane dalili zai janye wa wani, idan yasan cewa zai janye wa wani me zai sa ya je ya sayi fom din?.

Ya kara da cewa, baya tunanin jam'iyyar PDP zata bukaceshi da ya janye wa wani dan takara tunda itace da kanta ta sayar mishi da Fom.

Da yake magana akan abin da zai yi idan ya zama shugaban kasa, Jang yace, irin salon da ake amfani dashi na bita da kulli wajan yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya yana kashewa masu son zuba jari a kasarnan gwiwa, saboda da mutum ya bude kasuwanci sai a turomai EFCC su fara tambayrshi ina ya samo kudin?, Jang yace shi idan ya zama shugaba ba irin wannan tsarin zai yi ba, zai gyara hukumar ne ta yanda hukumomin kasa da kasa suke ya kuma habaka tattalin arzikin kasar.

No comments:

Post a Comment