Monday, 3 September 2018

Daga kan Messi ya kamata Barcelona ta kashe lamba 10>>Ronaldinho

Tsohon tauraron dan kwallon Barcelona, Ronaldonhi yayi kira ga kungiyar da cewa, daga kan Messi ya kamata su kashe lamba goma dan kada a kara samun me tabata.


Ronaldinho wanda Messi ya gaji rigar lamba goma daga gurinshi bayan da ya koma kungiyar AC Milan a shekarar 2008 ya bayyanawa The Sun cewa, idan Messi ya daina buga kwallo wanda ina fatan nan da wani lokacine me tsawo, ya kamata Barcelona ta kashe lamba goma ya zama babu wani dan wasa da zai sake sakata.

Ya kara da cewa, Messi ne wanda yafi kowane dan wasa yiwa Kungiyar bajinta a tarihinta kuma baya tunanin nan kusa za'a samu wanda zai canjeshi. 

No comments:

Post a Comment