Wednesday, 26 September 2018

Dan Gidan Obasanjo Ya Sha Alwashin Yi Wa Buhari Yakin Neman Zaben 2019

A cikin wata wasikar bazata da Abraham Obasanjo dan tsohon Shugaban kasar Nijeriya, Janar Olusegun Obasanjo ya aikewa daraktan watsa labaru na Ofishin yakin neman zaben shugaban kasa Buhari, Abraham Obasanjo ya jadda da goyon bayan shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da bayyana aniyarsa ta yiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe karo na biyu.


A cewar Abraham Obasanjo "Ina jaddada goyon bayana ga sake zaben shugaban kasa Buhari mai daraja da martaba a zaben 2019 dake tafe. Ina sanar daku aniyata ta yin aiki tukuru domin ganin Shugaban kasa Buhari ya sake cin zabe karo na Biyu.

Abraham Obasanjo, ya hori 'yan Nijeriya da su cigaba da marawa gwamnatin shugaban kasa Buhari baya domin cigaba da shimfida ayyukan alkairi wa al'ummar kasa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment