Monday, 3 September 2018

Dan takarar shugaban kasa ya nemi 'yan Najeriya su taramai Naira 200 dan ya sayi fom

A ranar asabar, 1 ga watan Satumba, Malam Hamidu Tafida, wanda ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, ya roki yan Nigeria da su yi masa karo karon 200 kowanne, don bashi damar siyen tikitin tsayawa takara.


Kamfanin dillancin labarai na NAN ta ruwaito cewa, Tafida ya yi wannan roko ne a Jalingo ya yin da ya ke kaddamar da kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasar.

"A yau ina farin cikin sanar da kudurina na tsayawa takarar shugaban kasar Nigeria. Bari na yi amfani da wannan damar, in roki akalla yan Nigeria Miliyan daya, da su yi karo karo na Naira 200 kowanne, su saya min tikitin tsayawa takara don bani damar cika alkawuran da na dauka" a cewar sa.

Tafida, wanda mataimakin darakta ne a karamar hukumar Jalingo da ke jihar Taraba, ya yi nuni da cewa, ya zamarwa yan Nigeria dole su kauracewa batagarin yan siyasa, don ganin dprewar ci gaban kasar.

Ya ce idan har haaka zabe shi, zai magance cin hanci da rashawa da kuma matsalar tsaro da tayiwa kasar katutu, kana zai samar da hanyoyin ci gaba a kasar. Dan takarar ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan yi ta hanyar farfado da masana'antu da kuma bunkasa fannin noma.

Ya shawarci al'umma da su yaki mummunar akidar nan ta siyen kuri’u, ya na mai cewa irin wannan dabi’a ce ke gurguntar da kasar.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment