Tuesday, 4 September 2018

Dan Wasan Fim, Bosho Ya Sa Wani Mara Lafiya Dariya Wanda Ya Shafe Wata Biyu Ba Ya Magana

Shahararran Dan Wasan Hausa Suleman Bosho, Wanda Ya Kware Wajen Wasan Barkwanci, Ya sa Wani Mara Lafiya Dariya, Bayan Mara Lafiyar Ya Shafe Fiye Da Watani Biyu yana Kwance A Asibiti Ko Iya Gane Wanda Yake Kanshi Ba ya yi.


Marar Lafiya Ya yi Hadari ne Tare Da Dan Uwansa A Hanyar Katsina. Tun Bayan Wannan Hadari Da Ya yi Yake Kwance A Asibiti Bai San Ina Yake Ba, Haka Zalika Bai San Wa Yake Kan sa ba, Haka Kuma Ba ya Magana, Fiye Da Tsahon Watanni  Biyu Yana Cikin Wannan Hali. 

Katsam Wata rana Sai Aka Ga Ya Bude Idanu Yana Murmushi, Aka Yi Mutukar Mamaki Sa'ar Da Aka Ga Yana Kallon Allon Talabijin, Ashe Fim Din Ciki Da Reno Aka sa A Wata Tasha.

Nan Take Farin Ciki Ya Lullube Mahaifiyar Wannan Yaro Inda Tace A Baya, Fata Take Yako Bude Ido Ya Dube ta Amma Abu Ya Gagara Sai A Sanadiyyar Fim Din Barkwanci Na Bosho.

Nan Take Aka Kirawo Likitan Dake Kula Da Mara Lafiyar, Zuwa Likitan Ke da Wuya Kan Yaron Sai Ya Cika Da Mamaki,  Nan Da nan Ya Shawarci Mahaifiyar Yaron Da ta Nemo Bosho A Duk Inda Yake Don Zai Taimaka Wajen Farfadowarsa. 

Ba tare Da Bata Lokaci ba Wani Ma'aikacin Gidan Talabijin Na Arewa 24 Mai Suna Muhammad Gwarzo, Ya Sanar Da Shahararren Marubucin nan Wato Nazir Adam Salihi, Batun, Shi ma Nan Da Nan Ya Nemo Suleman Bosho Ta Hannun Babbab Daraktanan Na Fim Din Barkwanci Wato Falalu A.  Dorayi. 

Cikin Ikon Allah Shi ma Bosho Ya Bada Hadin Kai Inda Suka Rankaya Zuwa Asibitin, Abin Mamaki Da Al'ajabi Suna Zuwa Asibitin Suka Sami 'Yan Uwan Mara Lafiyar Da Wayoyi A  Hannusu An Makare su Da Finafinan Bosho Suna Nuna Masa. 

Lokacin Da Bosho Ya Isa Gaban Gadon Da Yake Kwance Yana Kallon Saman Silin Na dakin, Zuru Babu Magana,  Allah Ne Ya san Karatun Kurma. Amma Bosho Na Zuwa Sai Ya Dafa Kafarsa Ya yi Masa Sannu Nan Da Nan Ya Dube Shi, Sai Murmushi Duk Da ba ya Iya Magana Amma Bakinsa Yana Murmushi Haka Nan Ya Fara Yunkurin Tashi, Yana Son Kama Hannun Bosho.

A Nan Take Bosho Ya Shiga Aikinsa, Ya fara Bada Labaran Barkwanci, Ba Mara Lafiyar Kadai ba, Duk Wanda Yake Wajen Sai Da Ya sha Dariya.

Lamarin Da ya sa 'Yan uwan Mara Lafiyan Da Mahaifiyar sa Suka ji  Dadin Ziyarar Da Bosho Ya kai Musu, Nan Take Suka fara Cewa Ashe Daman 'Yan Fim Suna Da Mutunci Da Amfani Haka A Cikin Al'umma. 

Shi kuma Suleman Bosho Ya yi Alkawarin Cigaba Da Ziyartar Mara Lafiyar Har Allah Ya Ba shi Lafiya.
Rariya

No comments:

Post a Comment