Thursday, 6 September 2018

Duk na yafe muku masu zagina>>Adam A. Zango

Bayan da ya saka labarin durkusawa a kasa yana neman afuwar Ali Nuhu, Adam A. Zango yayi bayanin cewa, ya daina yin rubutu wanda zai sa ma a zargeshi cewa da wani yake.


Adamu ya kara da cewa, ya yafewa duk masu zaginshi, Allah yasa afuwa ta zamo itace dabi'armu.

Ga abinda ya rubuta bayan saka hoton marigayi, Sheikh Jafar Adam.

"ALLAH YAJI KAN MALAM.... Allah kasa muzamo afuwa itace dabi"armu dan rasulinka Allah. Allahumma innaka afuuwun tuhibbul afwa fu affu anna. 
DUK NA YAFE MUKU MASU ZAGINA KUMA IDAN KUN LURA KO COMMENT WANDA ZATA SAKA AYI ZARGIN KO DA WANI NAKE YI NA DAINA TUNDA NA DAWO INSTAGRAM SABODA IN ZAUNA LFY......ALLAH YA YAFE MANA KURA KURANMU....YASA MU ZAMA MASU NEMAN AFUWA DA YAFIYA A TSAKANINMU__ALLAH YA SAKAWA SHU'AIBU KUMURCI DA ALKHAIRI."

No comments:

Post a Comment