Wednesday, 26 September 2018

Firayinministar New Zealand ta kafa tarihin kasancewa ta farko da ta taba zuwa da jaririnta taron MDD

Firayin ministar New Zealand, Jacinda Ardern ta kasance shugaba mace ta farko data taba zuwa taron majalisar dinkin Duniya da jaririyarta, Ardern tazo da jaririyarta 'yar watanni uku da haihuwa taron MDD ta ake yi a birnin New York ranar litinin din data gabata.


Mijinta da ya mata rakiya zuwa gurin taron ya rika mata rainon yarinyar a yayin da take gabatar da jawabi.

A watan Yuni daya gabatane Ardern ta zama shugabar kasa ta biyu da ta taba haihuwa tana kan karagar mulki sannan kuma ta farko da ta taba daukar hutun haihuwa a Duniya.

Ta bayyanawa manema labarai cewa a koda yaushe takan kasance da jaririyartata kuma tana shayar da ita mama ne shi yasa tazo da ita taron MDD, kamar yanda Buzzfeed ya ruwaito.

No comments:

Post a Comment