Wednesday, 5 September 2018

Fom din takarar APC ne mafi tsada a tarihin siyasar Najeriya: Anya jam'iyyar talakawace?


Ranar Laraba ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta soma sayar da fom ga masu son yin takara a inuwarta a zaben 2019.


Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar kan tsarin sayar da fom da gudanar da tarukan tsayar da 'yan takara ranar ta Laraba, ta ce za a soma sayar da fom ne sannan a kammala da taron zaben wanda zai yi mata takarar shugabancin kasa a ranar Asabar, shida ga watan Oktoba na 2019.

Sai dai babban abin da ya fi jan hankulan 'yan jam'iyyar da ma 'yan kasar baki daya shi ne tsawwalawar da APC ta yi kan kudin sayar da fom din neman takara.

Wani dan jam'iyyar da ke son tsayawa takarar majalisar dokokin tarayya a jihar Kano, Surajo Sani Marshall, ya shaida wa BBC cewa tun da ya soma harkokin siyasa bai taba ganin jam'iyyar da ta tsuga kudin sayen fom kamar APC ba.

"Ta yaya APC za ta sayar da fom din takarar majalisar dokokin tarayya kan N3,850,000 sannan ta ce ita jam'iyyar talakawa ce?," in ji Surajo Marshall.

Har yanzu dai APC ta ba bayyana dalilan ta na sanya wadannan makudan kudade a matsayin kudin sayar da fom.

Kudin sayar da fom:
Takarar majalisar jiha - N850,000
Takarar majalisar dokokin tarayya - N3,850,000
Takarar majalisar dattawa - N7,000, 000
Takarar gwamna - N22,500,000
Takarar shugaban kasa - N45,000,000.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment