Monday, 10 September 2018

Gamayyar Kungiyoyi A Kano Sun Sayawa Ganduje Fom Din Takarar Gwamna

A yau Litainin ne Kungiyar 'One2Tell10 Buhari Support Group - Kano Chapter' karkashin Coordinator din ta na jihar Kano wato Engr. Jazuli Abdulkarim Daiyabu da Sakataran ta na kasa Yuguda Abdul Aziz, Sun jagoranci sauran kungiyoyi wajen mikawa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje fom dinsa na takara. Wanda hadakar kungiyoyin suka saya masa.


Wadannan kungiyoyi ne dake mara baya ga shugaba Buhari da gwamnan Kano Ganduje, kuma sun mika wannan fom din da kudin sa ya kai kudi kimanin naira miliyan 22,500,000 wanda aka saya a ofishin jam'iyyar APC ta hannun shugaban ta na jihar Kano Alh. Abdullahi Abbas da sauran shugabanni.

Bayan nan aka damkawa gwamna fom din a fadar sa dake gwamnatin jihar Kano a babban dakin taro na Coronation Hall, kuma taron ya samu halarar masu ruwa da tsaki na gwamnatin jihar Kano tare da manyan daraktoci da coordinators na kungiyar One2Tell10 BSG na kananan hukumomi 44 da dubban magoya bayana wadda AB Baffa Bichi shi ne Daraktan ta na kasa baki daya.
rariya.

No comments:

Post a Comment