Tuesday, 4 September 2018

Gerard Pique ya koma hawa mashin dinshi na naira miliyan 4 zuwa gurin atisaye bayan da aka hanashi hawa mota

Kudi masu gida rana, dan wasan Barcelona, Gerard Pique na fuskantar hukuncin hana hawa mota bayan da aka kamashi yana tuki da lasisin tukin daya daina aiki, wannan dalili yasa ya koma hawan mashin dinshi me amfani da hasken rana da ake sayarwa akan kudi kimanin Naira miliyan 4.Pique na amfani da wannan mashin wajan halartar wajan atisaye.

Wani kamfanin kera baburane ya baiwa Messi da Fabregas da Pique din kyautar wannan babur me dauke da sunayensu.

Bayan kamashi da laifin, ancishi tarar kudi sannan aka sakashi koyan aiki da dokokin hanya na tsawon awanni 24,koda a kwanakin baya sai da aka kama Pique da laifin tuki rike da dansh.

No comments:

Post a Comment