Friday, 7 September 2018

Gwamna Ganduje da Shugaban APC sunje zawarcin Shekarau har gida

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole rakiya zuwa gidan tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau inda suka yi zawarcin shi dan ya dawo jam'iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa, Malam Ibrahim Shekarau ya gayawa Gwamna Ganuje da Oshimhole cewa, zai yi nazari akan wannan lamari kuma nan bada dadewa ba zai bayyana ra'ayinshi.

Gwamna Ganduje da yake jawabi a gurin, yace, da mutane irin su shekarau a jam'iyyyar APC babu abinda zai hanasu samun nasara.

No comments:

Post a Comment