Wednesday, 12 September 2018

Gwamnan Fayose zai mika kansa ga hukumar EFCC

Gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, Ayodele Fayose, ya ce da zarar ya sauka dsaga mulki zai mika kan sa ga hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta kasar, EFCC.


EFCC na zargin gwamnan da sace wasu kudade na jihar.

Ranar 15 ga atan Oktoba ne Gwamna Fayose zai sauka daga mulki bayan ya kammala wa'adinsa na biyu - ba a jere ba- na shugabancin jihar.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata da yamma, ya ce "jiya na mika wasika ga EFCC inda na shaida mata bukatata ta mika kai na a gare ta ranar Talata 16 ga watan Oktoba da misalin karfe daya na rana domin na yi bayani kan wasu batutuwa ko na amsa tambayoyin da nake da masaniya a kansu."No comments:

Post a Comment