Wednesday, 5 September 2018

Gwamnatin Buhari akwai rashin tattali: Ta yaya zaku bayar da kyautar dala miliyan dari 322 sannan ku ciwo bashin dala miliyan dari 328?>>Atiku Abubakar

Fadan cacar baki ya barke tsakani  tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabacin kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da mataimakin shugaban kasa me ci, Farfesa Yemi Osinbajo akan canja fasalin kasa.


Atiku Abubakarne ya fara wallafa rubutunshi a jaridar Premiumtimes inda ya bayyana cewa Osinbajo baya goyon bayan canja fasalin kasa, Osinbajo shima ya mayar da martani inda yace ba haka abin yake ba akwai kalar canja fasalin kasa da baya goyon baya amma ba gaba dayan shi bane yake suka.

Saidai Atiku ya sake mayar da martani ga Osinbajo inda yace, kawai ya fito ya fadi cewa yana goyon bayan canja fasalin kasa ko kuwa baya goyon baya? Sannan Atikun ya kara da cewa, a cikin bayanin da Osinbajo ya wallafa akwai inda yace suna tattalin dukiyar kasarnan.

Atiku yace, ina dabarar baiwa 'yan Najeriya kyautar dala miliyan dari 322 na Abacha da gwamnati tayi kwanannan, gashi kuma wata daya bayan hakan kun ciwo bashin dala miliyan dari 328? Atiku yace wannan rashin tattaline

No comments:

Post a Comment