Friday, 28 September 2018

Hadarin jirgin saman Abuja: Anyi jana'izar sojan da ya rasu: Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hannun me magana da yawunshi, Malam Garba Shehu ya mika ta'aziyyarshi ga jami'an sojin kasarnan bisa rashin da suka yi na ma'aikacinsu a hadarin jirgin sama a yau, Juma'a.


Shugaba Buhari ya bayyana sojan, Bello Baba Ari a matsayin gwarzo wanda baza'a manta dashi ba haka kuma ya bayyana cewa ba za'a manta da iyalinshi ba, za'a basu duk taimakon da ya kamata.

Shugaba Buhari ya kuma jajantawa sojoji biyu da suka samu raunuka a wannan hadari da ya faru yau.

An yi jana'izar Bello Baba Ari wanda shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari ya halarta.

No comments:

Post a Comment