Thursday, 27 September 2018

Hotunan yanda sa'insar Mourinho da Pogba ta kasance

A jiyane rahotanni suka bayyana cewa, me horas da 'yan wasa na kungiyar Manchester United, Jose Mourinho da dan wasan kungiyar, Paul Pogba sun samu sabani inda har sukayi sa'insa tsakaninsu a gurin atusaye bayan da yaki saka Pogba din a wasa sannan kuma ya kwace mataimakin Kyaptin daga hannunshi.


Mourinhon ya tabbatar da kwace mataimakin kyaptin din daga hannun Pogba saidai ya musanta cewa akwai tsama tsakaninshi da dan wasan.

Wadannan hotunan sun nuna yanda sa'insar tsakaninsu ta kasance.

No comments:

Post a Comment