Tuesday, 4 September 2018

Ibrahim Shekarau ya koma APC

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya yanke shawarar barin jam'iyyar PDP zuwa APC, rahotanni sun bayyana cewa Shekarau ya gana da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje dan shirya komawar tashi APC a bayyane.


Me magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule ne ya bayyanawa jaridar Daily Trust haka a yau, Talata inda yace Shekarau ya gana da gwamna Ganduje jiya a Abuja sannan yana shirin ganawa da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC kamin ya fito ya bayyanawa Duniya aniyar tashi.

Sule yace, shekarau ya dauki wannan mataki ne saboda rashin adalcin da PDP ta mishi da kuma kokarin baiwa bangaren Kwankwaso fifiko da jam'iyyar keyi wanda ba zasu amince da hakan ba.

Ya kara da cewa, Shekarau ya tuntubi magoya bayanshi kamin ya yanke wannan shawara.

No comments:

Post a Comment