Thursday, 27 September 2018

INA MA ACE

Ina Ma Ace yadda Shugabannin Najeriya ke haukacewa akan komawa kujerar mulki haka suke haukacewa akan matsalolin kasar. 

Ina Ma Ace yadda muke damuwa da wane ya ci zabe wane kuma ya fadi haka muke damuwa da son ci gaban kasar mu. 

Ina Ma Ace yadda ake sukar wasu 'yan siyasa akan ba wa 'ya'ya da surikansu takara, a samu wani yana shan yabo saboda tsayar da 'ya'yan Talakawa. 

Ina Ma Ace yadda muke yawan sukar shugabanni haka muke yawan ambaton Allah da neman gafarar Sa. 

Ina Ma Ace yadda muke yawan farautar laifukan juna gami da yada su haka muke yawan yada hanyoyin kyautata rayuwar mu. 

Ina Ma Ace Yadda muke yawan kare muradin 'yan siyasa, haka muke yawan son taimakon raunana daga cikin mu. 

INA MA ACE.... 

Allah Ya Sa Mu Dace.
Maje El-hajeej Hotoro.

No comments:

Post a Comment