Tuesday, 4 September 2018

Ina nan daram PDP>>Malam Ibrahim Shekarau

Wannan shine jawabin da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi kan rashin ficewarsa daga jam’iyyar PDP.


"Ni Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, ina kara godiya ga Allah Madaukakin Sarki mai kowa mai koma.

"A yanzu dukkan jama’armu suna sane da dukkan fadi tashi da suke faruwa a jam’iyyarmu ta PDP a jihar Kano, inda Sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa ta bada sanarwar rushe shugabancin jam’iyya na jihar Kano. Wanda kuma tuni muka kalubalanci wannan hukunci, muka nuna rashin amincewarmu dashi, domin yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP.

"Tun faruwar wannan al’amari muna ta tattaunawa a tsakankaninmu mu jagorori da iyayen jam’iyyar PDP na jihar Kano domin daukar matakin da ya dace, sanin kowane cewa a tsarin tafiyarmu bama yanke kowane irin hukunci akan kowane irin al’amari sai mun tuntubi dukkan sassa na abokan tafiya.

"Muna nan muna cigaba da irin wannan tuntuba da tautanawa, don haka muna kira ga al’ummarmu da su kara hakuri in lokaci yayi za’a ji bayani daga bakin mu kai tsaye inda zamu yiwa jama’armu cikakken bayani na dalilin mu na yanke kowane irin hukunci da muka dauka.

Muna rokon Allah yayi mana jagora cikin dukkanin ayyukanmu, Muna rokon Allah ya kara rufa mana asiri duniya da lahira".
Rariya.

No comments:

Post a Comment