Friday, 28 September 2018

Ina so in haihu da yawa nima in dauki irin wannan hoton>>Dan majalisa Abdulmumini Jibril

Dan majalisar wakilai, Abdulmumini Jibril ya saka wannan kayataccen hoton iyalin a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya bayyana cewa ya kayatar dashi sosai kuma wata ran shima zai so ya dauki irin wannan hoto da iyalinshi.


Ya kara da cewa, yana so ya haihu da yawa kuma ya kagara yaga ranar da zai dauki irin wannan hoto shima, a karshe ya yiwa wannan iyali fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment