Saturday, 15 September 2018

'Indai Buhari ya zarce to ni kuma lahira zan zarce'

Da alama dai akwai wadanda suka gaji da mulkin shugaba Buhari da yawa, a shekaran jiyane mukaji labarin wani matashi da ya dare kan tangaraho/karfen sabis yace bazai sauko ba sai Buhari ya sauka daga mulki hakama a jiya munji wata mata da tace ba zata haihu ba itama sai Buharin ya sauka.


A yau kuma wannan matashinne da shafin Northernblog suka wallafashi inda yake kwance a cikin makara, ya fadi cewa idan dai Buhari ya zarce to shima lahira zai zarce.

To sai muce Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment