Thursday, 6 September 2018

India ta halatta yin luwadi da madigo

Kotun koli a India ta halatta yin luwadi da madigo a kasar, matakin da aka dade wasu na adawa da shi.


Kotun ta halatta yin hakan ne ga manya da suka mallaki shekarun girma.

Hukuncin dai ya yi wa masu gwagwarmayar kare 'yan luwadi da madigo dadi inda suka rungume juna suna murna bayan zartar da hukuncin.

Alkalai biyar ne suka yi nazari game hukuncin da aka yanke a shekarar 2013.

Tsohuwar dokar tun zamanin turawan mulkin mallaka da aka fi sani da sashe na 3-7-7 ta zartar da hukuncin duk wanda aka samu da yin madigo da luwadi za a yanke masa hukuncin ko dai sama da shekara 10 a kaso.

Tun da farko ma su fafutuka sun ce ayyana auren jinsi a matsayin laifi, zai zama babbar barazana ga 'yancin masu ra'ayin auren jinisi daya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment