Wednesday, 5 September 2018

INEC ta wa mutane miliyan 5 rigistar zabe a Kano

Hukumar zabe ta jihar Kano, ta bayyana cewa, ta yiwa mutane sama da miliyan 5 rigistar katin zabe da ake sa ran zasu kada kuri'arsu a zaben shekarar 2019 me zuwa.


Jaridar The nation ta ruwaito me magana da yawun hukumar, Alhaji Garba Lawal Muhammad ya bayyanawa manema labarai haka, ya kara da cewa, yawan wadanda aka yiwa rigistar zai iya canjawa idan suka kammala hada bayanai.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka yi rigistar katin zaben su a shekarar 2011 da 2014 da 2017 da basu amshi katunan zaben nasu ba su zo su amsa .

No comments:

Post a Comment