Monday, 10 September 2018

Jami'ar Dutse ta koyar da yanda ake alawar Dinya

Bayan gudnar da bincike game da alfanun sanar sarrafa ‘ya ‘yan bishiyar Dinya da ganyen ta wadda aka kwashe shekaru aru-aru anayi a kasar Hausa, wadda kuma a ‘yan shekarun nan ta kama tafarkin durkushewa. Hukumomin Jami’ar tarayyar dake Dutse sun bullo da tsari na musamman ga mata da matasa na ‘kauyen Rajun Dinya kan sabuwar fasahar farfado da wannan sana’a mai tarihi.


Farfesa Fatima Batul Umar dake zaman shugabar jami’ar tarayya ta Dutse ta fayyace dalilin bullo da sabuwar fasahar. Inda ta ce sun bullo da wannan shiri ne domin al’ummar dake yankin su amfana

Malam Mati Garba shugaban matasan da suka koyi sabuwar fasahar cewa ya yi wannan ilimi da suka samu ya taimaka musu sosai da sosai, saboda sun fahimci cewa a baya basu san yadda ake sarrafa Dinyar ba.

Mataimakin gwamnan Jigawa Barrister yace zasu tallafawa wannan yunkuri na Jami’ar tarayya ta Dutse na habaka tattalin arzikin iyali.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment