Friday, 14 September 2018

Ka lura Idan zaka gaisa da 'yan siyasa ka rika saka safar hannu>>Sanata Shehu Sani ya baiwa sabon shugaban DSS shawara

Sanata Shehu Sani ya taya sabon shugaban hukunar 'yansandan farin kaya, DSS, Yusuf Magaji Bichi murnar mukamin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nadashi yayi kira a gareshi da yayi kokarin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a kasarnan.


A karshe Sanata Shehu Sani ya baiwa Yusuf shawara da cewa ya lura idan zai gaisa da 'yan siyasa ya rika saka safar hannu.

No comments:

Post a Comment