Wednesday, 26 September 2018

Kadan ya hana amin aure ina 'yar shekaru 13>>Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta bayyana yanda ta sha da kyar a wani yunkuri da aka yi na mata aure lokacin tana karamar yarinya 'yar shekaru 13.


Vanguard ta ruwaito Rahama Sadau lokacin da ake tamyarta me tayi ko kuma me take tunin ya kamata ayi na ilmantar da yara mata da kuma hana yi musu auren wuri a Arewacin Najeriya?.

Rahama tace, wasu daga cikinsu suna yaki da maganar yiwa yara mata auren wuri da kuma karantar dasu duk da cewa maganace me sarkakkiya saboda da an tabo maganar auren wuri to addini zai shigo ciki.

Tace a nata bangaren tana zama da iyayen yara tana wayar musu da kai, kuma itama kadan ya hana a mata auren wuri tun tana 'yar shwkaru 13 da haihuwa. Tace abubuwa da yawa sun faru amma suna iya bakin kokarinsu.

Da aka tambyeta ta yaya ta tsallakewa maganar yi mata auren a wancan lokaci?, sai tace a koda yaushe tana godewa mahaifiyarta saboda tana so su cimma burin rayuwarsu.


No comments:

Post a Comment