Saturday, 29 September 2018

Kalli hotunan Zainab Indomie na da dana yanzu

A kwanakin baya da aka daina jin duriyar tauraruwar fina-finan Hausa, Zainab Indomie an rika ganin hotunanta dake nuna kamar tana cikin wani mawuyacin hali da kuma suka rika sanya alamun tambaya a zukatan masoyanta.

A cikin kwanakinnan Zainab ta fito ta bayyana cewa ta dawo zata ci gaba da yin fim kuma abokin aikinta, Adam A. Zango ya matukar taimaka mata akan hakan kamar yanda shi da ita duk suka bayyana a shafukansu na sada zumunta.

Wannan hoton na sama Zainab din ce a lokacin da take cikin irin wancan mawuyacin halin da kuma yanzu da ta murmure, kamar yanda Adam A. Zango ya saka a dandalinashi na sada zumunta.

No comments:

Post a Comment