Tuesday, 25 September 2018

Kalli irin sakon taya murnar ranar haihuwa da tsohon mijin Samira Ahmad, T.Y Shaban ya aike mata dashi

A yayin da tauraruwar fina-finan Hausa, Samira Ahmad tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta a jiya, Litinin, wani abu da ya dauki hankulan mutane shine irin yanda tsohon mijinta kuma tauraron fina-finan Hausa, T. Y Shaban ya aika mata sakon taya murna na musamman.Shaban ya bayyana cewa, ina tayaki murna Samira Ahmad, 'yar kucila. Ina miki fatan Alheri da samun ingattacciyar rayuwa anan gaba.
Wannan sako yasa wasu daga cikin masoyansu suka rika kira da cewa ya kamata su maida komai ba komai ba su sasanta kansu su koma rayuwarsu ta aure.

No comments:

Post a Comment