Monday, 17 September 2018

Kalli jaririyar da aka haifa da ido a tsakiyar goshi kuma babu hanci

Ikon Allah ya wuce mamaki, wata mata 'yar kasar Indonesia ce ta haifi jaririya da ido a tsakiyar goshinta sannan kuma babu hanci, matar ta haihune a ranar Alhamis din da ta gabata kuma ta haihune da kanta ba tare da taimakon likitoci ba.


Saidai awanni 7 bayan haihuwar jaririyar ta koma ga mahaliccinta.

Likitoci sunyi kokarin ganin ceto rayuwarta inda aka sa mata numfashin nan na bature ta baki tunda babu hanci, inji daya daga cikin likitocin asibitin da aka haifeta, amma duk da haka bata rayuba, likitan me suna Dr Syarifuddin Nasution ya shaidawa manema labarai cewa irin wadannan jarirai yawanci ta hanyar yin tiyata ake haifarsu amma cikin ikon Allah sai gashi ita, Suriyanti, mai jegon, ta haihu da kanta.

Yace duk da cewa dama basu yi tsammanin jaririyar zata rayuba amma da ace ta rayu din da zasu mikata babban asibitine dan ci gaba da duba lafiyarta.

Ya kara da cewa, sanadiyyar haihuwar irin wannan jarirai shine ta'ammuli da sinadarin Mercury, maijegon da mijinta sun kasance a can wani kauyene na kasar inda suke aiki da wani kamfanin hakar ma'adanai.


No comments:

Post a Comment